Kamfanin Facebook ya fitar da sanarwar shirin fitar da wata sabuwar fasahar hotan bidiyo ta 360-degree. Wanda hakan ke nufin masu kallon hoton bidiyon da akeyi kai tsaye a shafin Facebook, zasu iya kallon kowacce kusurwa idan suka so hakan.
Watsa shirye-shirye ta hanyar Facebook live ya zamanto wata gagarumin abu ga dandalin Facebook, a kokarin da kamfanin yake na ganin harkokin mutane na karuwa a shafin. Shugaban kamfanin Mark Zukerberg, yace kamfanin na shiga wani karni ne na watsa hotan bidiyo kai tsaye.
Facebook ya mayar da hankali ne ga duk wata sabuwar fasaha da ta kunshi hotunan bidiyo. Sai dai kuma ba Facebook kadai bane ke mayar da hankali ga fasahar hotunan bidiyo, sauran kamfanoni kamar su Google da Samsung baki dayansu ba a barsu a baya ba.
Yanzu haka dai masu yin Facebook live ne kadai zasu iya amfani da wannan sabuwar fasaha, wato har yanzu dai ba a bude ta ga sauran masu shafukan Facebook ba tukunna. Sai dai ana kyautata zaton Facebook zai kaddamar da wannan fasaha ga sauran mutanen nan bada dadewa ba.
Your browser doesn’t support HTML5