Ranar Matasan Afirka - Matasan Jamhuriyar Nijer Sun Koka Iya Matuka

Alkalumman kididdiga akan yawan jama’ar Nijer sun yi nuni da cewa sama da kashi %70, cikin dari na al’ummar kasar duk matasa ne, abinda ke fayyace gudummuwar da wannan rukuni na matasa ke da shi wajan ayyukan ciyar da kasar gaba.

Sai dai wani abinda ke zama tarnaki ga matasan kasar ta Nijer shine, rashin samun kulawar da ta dace a gwamnatance, ta hanyar la’akari da cewcar kashi daya cikin dari kacal ake cirewa sha’anonin matasa a kasafin kudin kasar na kowace shekara.

Alityu Umar, shine shugaban majalisar matasa ta Nijer, ya ce yin hakan yana matukar ragewa matasa hanzari.

Koda shike gwamnatin tana nuna damuwa akan halin da matasan kasar ke ciki, amma kuma cewa take yi sauwun giwa ya take na Rakumi, domin a cewar ministan matasa Kasim Mukhtar, halin da ake ciki a yau hankalin hukumomi ya karkata ne wajan ayyukan samar da tsaro, lamarin da yayi sanadiyyar lakume babban kason kasafin kudin kasar a ‘yan shekarun baya bayan nan.

Ya ce mayar da hanakali akan sha’anin tsaro nada matukar muhimmanci amma warware matsalolin matasa ma ba baya ba, kuma yayi kira da jan hankalin shugabannin Afirka su dubi harkokin matasa da idon basira.

Domin Karin bayani ga cikakken rahoton Sule Mumini Barma daga jamhuriyar Nijer.

Your browser doesn’t support HTML5

Matasan Jamhuriyar Nijer Sun Koka Iya Matuka