Dandalin VOA ya yi duba ne dangane da fim din Mutum Da Aljan, inda muka zanta da marubuci kuma wanda ya shirya fim din wato Murtala Balarabe Baharu dangane da dalilan da ya sa ya sanya camfi da iskokai a fim din nasa
Murtala Baharu ya ce jigon fim din ya yi waiwaye ne ga dabi’ar nan ta shafar aljani ga jikin bil adama, tare da nuna hanyoyin da hakan ka iya afkuwa.
A fim din Mutum da Aljan, mai shiryin fim din ya nuna yadda malam Bahaushe ke yarda da camfi da iskokai da hanyoyin daukarsu da ma yadda za’a kare kai daga kamu da shafarsu.
Baharu ya kuma nuna al’adar mafarauta da zaman gidan gandun tare da iyaye da 'yan uwa, inda ya kara fito da yadda 'yan boko ke kin amincewa da wasu daga cikin al’adun malam Bahaushe.
A fannin mu na tsegumi kuwa Fitatticiyar jarumar nan ta Nollywood Ini Edo da mawakin nan Sammie Okposo sun bayyana cewar daga ranar 30 ga oktoban 2016 sun sauka daga jakadancin kamfanin sadarwn da suke yi daga jerin jakadancin kamfanin .