Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Glo Ya Fadada Fasahar 4G LTE Zuwa Garuruwa 33


Biyo bayan kaddamar da fasahar laluben yanar gizo ta 4G LTE me sauri, kamfanin sadarwa na Globacom yace ya fadada wannan fasaha har zuwa garuruwa 33 a fadin Najeriya.

A baya bayannan ne kamfanin sadarwar ya samar da wannan fasaha a wasu jihohi har 12 wadanda Uku daga cikinsu suka hada da jihohin Arewa, wato babban birnin Tarayya Abuja da Jos ta jihar Plateau da kuma Yola ta jihar Adamawa.

A lokacin kaddamar da wannan fasaha ta 4G LTE, kamfanin Globacom yace wannan zai taimaka masa wajen karfafa alkawarinsa na ganin cewa ya fadada fasahar zuwa sauran birane a fadin Najeriya.

4G LTE fasaha ce da wayoyin zamani smart phones a turance ke amfani da ita wajen samun network mai karfi da sauri. 3G LTE itace fasahar da ake amfani da ita a Najeriya kafin fitowar 4G LTE.

Cikin manyan abubuwan da duk masu layin Globacom da ke da fasahar 4G LTE zasu mora kyauta, sune Miliyoyin wakoki da hotunan bidiyo da fina finai.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:04 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG