Manta baya shine babbar matsalar dake addabar abota, a wannan zamanin da muke ciki da maza da mata baki daya.
Halima baba Ahmed, wata mai gwagwarmaya akan ‘yancin yara ne ta bayana haka a wata tattaunawar da suka yi akan abota baya daya daga cikin abokan ya samu ko ta ta samu wani sabon daukaka.
Ta kara da cewa hali shine shedar mutuntaka, amma jahilici da son zuciya kan taka mahimmirar rawa a wannan fanin.
Ita kuwa Aisha Dika , ‘yar jarida cewa tayi abokan gaskiya suke fadin gaskiya komai dacinta domin a kowane lokacin suna kallon yadda aka faro tun lokacin da ake kanana bada wani daukakar da aka samu a yau ba.
Hajiya Adama Aminu Gurim, cewa tayi rashin hangen nesa da rashin fadawa juna gaskiya shim aba karamin tasiri yake yiba wajen tabarbarewar dangantaka tsakanin abokai.