Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashe "50" A Fadin Duniya Da Su Kafi Saukin Rayuwa Dan Zama!


A wani sakamakon bincike da wata hukuma mai zaman kanta ta gabatar, don gano kasashen da su kafi saukin rayuwa a fadin duniya. “Numbeo” hukumace da kan tattara bayanan al’umma da kuma tafiye-tafiye daga wata nahiya zuwa wata.

Sun bayyanar da wasu kasashe da sukafi saukin rayuwa, wanda su kayi amfani da wasu alkalumma wajen tsamo kasashen. Wasu daga cikin abubuwan da su kayi amfani da su, sun hada da rashin tsadar gidan haya, saukin kayan abinci, yawan gidajen abinci masu sauki, da dai wasu abubuwa makamantan hakan.

Kasar Indian itace kasa da tafi saukin rayuwa a duniya, sai jerin sauran kasashen da suka hada da, Moldova da ke yankin gabashin kasashen turai, Pakistan, Kazakhstan, Nepal, Ukraine, jihar Georgia ta Amurka, Algeria, Azerbaijan, Colombia, Tunisia, Macedonia, Syria, Serbia, Albania, Sri Lanka, Bosnia da Herzrgovina, Philippens, Afrika ta Kudu, Romania, Mexico, Armenia, Bangladesh.

Kasar Morocco, tabiyo baya, kana kasar Indonesia, Bukgaria, Masar, Bolivia, Malaysia, Botswana, Peru, Russia, Poland, Brazil, Belarus, Montenegro, Vietnam, Libya, Namibia, Kenya, Thailand, Iran, Hungary, Jamhuriyar Czech, El Salvador, Fiji, Chile, Guatemala, Ethiopia, a karshe sai kasar Ecuador.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG