An Gano Girgijen "Oyster Nebula" Wanda Yake Bama Taurari Haske!

Girgijen Dake ba Taurari Haske

Wani jirgi kirar “Soyuz TMA-20M” ya sauka a wannan duniyar, bayan kwashe kwanaki dari da saba’in da biyu 172, da yayi a sararrin samaniya. Dauke da ma’aikatan hukumar binciken sararrin samaniya NASA. Ma’aikatan hukumar arba’in da takwas 48, ne suka tafi sararrin samaniyar don gudanar da wani bincike.

Ma’aikatan sun hada da na kasa-da-kasa, da suka ziyar ci duniyar sama, a lokacin binciken nasu, daya daga cikin kyamarorin da suka tafi da su, ta dauki hoton wata hallita da ta bayyana, a matsayin hallitar da ke bada haske ga taurarri da wata, mai suna “Oyster Nebula” wadda a kafi sani da “NGC 1501.”

Ita dai wannan hallitar tana kama da girgije, wanda idan ta haska taurari, sai su dinga bada wasu nau’in kaloli na daban, wanda za’a iya ganin taurari kan canza kala daga lokaci zuwa lokaci. Kana halittar na yawo zuwa wajaje daban-daban, da yasa wasu lokutta ba’a ganin hasken taurari idan yanayi ya canza.