Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar JAMB Da NUC Sun Kudiri Aniyar Warware Matsalolin Bada Guraben Karatu


Hukumar JAMB ta bayyana shirinta na aiki kafada da kafada tare da hukumar dake kula da jami’o’in Najeriya domin warware matsalolin da manyan makarantun gaba da sakandire ke fama da su wajan aikin bada sababbin guraben karatu na bana.

Shugaban hukumar farfesa Ishaq Oloyode, ya bayyana haka ne a ranar juma’ar data gabata a birnin Abuja yayin da yake marabtar sakataren hukumar da ke kula da jami’o’in Najeriya farfesa Abubakar Rasheed wanda ya jagoranci tawagar sa.

Oloyode ya bayyana cewa hukumar jarabawar da hukumar da ke kula da manyan makaratun sun kasance manyan ma’aikatun gwamnati biyu da alhakin bada guraben karatu a manyan makarantun gaba da sakandire a wuyansu kuma dole su yi aiki kafada da kafada domin tabbatar da samar da ingantaccen ilimin gaba da sakandire.

A nasa bangaren, Rasheed ya bayyana cewa dalilin ziyarar shine a kara karfafa dangantakar dake tsakanin hukumomin biyu domin a tabbatar dadaukar daliban da suka can canta.

Daga karshe Oloyode da Rasheed, sun taya juna murnar akan ayyukan nasu, da kuma mika tabbacin ciyar da harkokin ilimi gaba.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG