Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shafin Instagram Ya Samo Hanyar Rufe Kalaman Batanci Da Mutane Ke Rubutawa


instagram
instagram

A jiya Litinin ne shafin sada zumunci ta hayar kafe hotuna na Instagram, wanda yake mallakar kamfanin Facebook ya gaddamar da wata manhaja da zata baiwa mutane dama su rika kula da kalaman da mutane ke ajiye musu kan hotunan da suka kafe.

Wannan manhaja zata baiwa masu shafin damar rubuta wasu kalmomi da suke ganin basu da kyau ko na batanci ne, haka kuma duk wasu kalamai da wasu suka rubuta idan har sun kunshi kalmomin to ba zasu fito ba.

Kalamai irin na batanci akan gansu kan shafukan sada zumunci na yanar gizo, wanda suka hada da Facebook da Instagram da Twitter, hakan yasa wasu shararrun mutane da sukayi fice a duniya ke rufe shafunansu dalilin ire iren kalaman da ake rubuta musu na batanci.

A baya bayan nan ne Twitter ta rufe shafukan wasu mutane na har abada, a sanadin kalaman cin zarafi da sukayi tayiwa wata jarumar fina finai mai suna Leslie Jones, wanda har yasa ta rufe shafinta saboda cin mutuncin yayi yawa.

Wannan sabuwar manhajar dai ta zo ne kusan wata guda bayan da mawakin nan Justin Beiber ya bar dandalin Instagram bayan da yayi barazanar rufe shafinsa ga al’umma biyo bayan wani hoto da ya kafe, mutane sukayi ta rubuta masa kalaman batanci.

Yanzu haka dai shafin Instagram ya baiwa mutane damar goge kalaman da aka rubuta musu, kuma zasu iya sanar da duk wani cin zarafi da hana wanda ya aikata irin wannan hali ganin shafinsu. Amma yanzu da wannna sabuwar manhajar zasu iya rubuta jerin kalmomi marasa kyau, wanda Instagram zai iya zakulo duk wasu kalamai masu kunshe da kalmomin ya boye su.

XS
SM
MD
LG