Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matakan Kariya Ga Ciwon Kansa A Matakin Farko!


Cutar Kansa
Cutar Kansa

Alamomi biyar da kan bayyana ma mutun cewar yana dauke da cutar “Cancer” Kansa ciwon daji, idan ana maganar ciwon daji, daukar matakan kariya shine abu mafi mahimanci a dai-dai lokacin da aka ga wadannan alamun.

A wani bincike da aka gudanar da ya nuna cewar, mutane da dama basu daukar wadannan alamun da muhinmanci, domin suna ganin kamar ba wani abu ne da za’a damu da suba. Wasu kuwa basu da masaniyar cutar kansa a matakin farko.

Abubuwa da mutane ya kamata su mai da hankalin su, wajen riga kafin cutar Kansa sune, duk lokacin da mutun yake rama batare da wani dalili mai karfi ba, ko mutun ya samu wani gwalando da yaki warkewa, yana da kyau mutun yaga likita.

Ga matasa idan aka fara samun tari mara kaukautawa, ko fashewar muryar mutun, ta kara kara ko sanyi, shima alamu ne na kansa, haka idan mutun na yawan samun daurewar ciki, ko ‘yan mata da lokacin al’adar su, su kan yi ciwon ciki da yake wuce kwana biyu zuwa uku, to su nemi ganin likita.

Haka idan mutun ya yawaita shiga bayi, batare da cin abinci mai yawa ba, ko mutun yayi aman jini, fitsari ko kashi duk dauke da gudan jini, ko a samu mutun yana yawan fitar jini ta hancin shi.

Duk wadannan alamu ne na cutar Kansa, wanda yake da muhimanci idan mutane zasu gaggauta zuwa asibiti, don ganin likita, hakan zai taimaka wajen shawo kan cutar tun a matakin farko.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG