A yayin da Musulmi a fadin duniya ke ci gaba da gudanar da bukukuwan sallah, wasu matasa a jihar Legas sun sa kawunan su cikin wani hali inda har daya daga cikinsu ya rasa ransa.
Matashin me suna Onyibo, da sauran abokansa sun shiga gasar shan gwaggwaro ne, lamarin da yayi sanadiyyar rasuwar matashin a yayin da ya fara aman jini a lokacin gasar.
Wani jami’in ‘yan sanda ya bayyanawa manema labarai cewa an tsinci gawar matashinne a wani gareji inda sauran abokan nasa suka jefar da gangar jikin suka arce sakamakon tsoron kada jami’an tsaro su kama su.
A cewar jami’in, wani ganau wanda ya nemi a bayyana sunan sa ya bayyanawa jami’an ‘yan sandan cewa ana yawaita ganin matsahin da abokan nasa buge da giya a kan layukan unguwar. Ya kara da cewa “a lokacin da suke cikin shan giyar ne Onyibo ya fadi kasa, da abokan suka yi kokarin daga shi suka ga alamun ya fara aman jini sai suka dauke shi suka bar gurin da shi”.
Daga karshe ya bayyana cewa da suka kasa farfado da shi ne yasa suka jefar da shi suka gudu.