Inda Wani Yayi Rawa Ya Samu Kudi! Wani Idan Yayi Sai Buzun Shi!

Rubutun Bango

Wasu dabi’u da a wasu kasashe ba wani abu bane, amma a wasu kasashen, idan mutun yayi su zasu jefa shi cikin fitina. A kasar Austrlia, karya doka ne mutun ya manna wani hoto, ko yin rubutu a jikin wani gini, ko dai na wani mutun ko na gwamnati. Yin hakan zai sa a yanka ma mutun tara da zata kai $380 wanda tayi dai-dai da naira dubu dari da hamsin, ko gidan wakafi.

A kasar Singapore, babban laifi ne, mutun ya dinga amfani da damar yanar gizon makoci “Wi-Fi” idan kuwa aka samu mutun da wannan aika-aikan, za’a yanka mishi tara da takai $10,000 dai-dai naira milliyan hudu, ko kuwa mutun yaje gidan yari na wasu shekaru.

Hakama a kasar Birtaniya, idan mutun ya saka na’urar bayyana barawo, kodai na gida ko na mota, da zai dinga kara batare da kaukautawa ba, hakan zai sa a yanke ma mutun tara da tana iya kaiwa $6,500 kimanin naira milliyan biyu da dubu dari biyar.

A kasar Amurka, kuwa karya doka ne a samu mutun ya saukar da wandon shi kasa, yana tafiya akan titi, wanda hakan zai bayyanar da wani bangare na jikin shi, hakan zai sa a yanke ma mutun tara na $1,000 wanda tarar na iya kaiwa naira dubu dari hudu, ko kuma mutun yaje gidan yari na wasu watanni.