Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amfani Da Fasahar Bayyana Hotuna Ta Surori Uku Da Makaho Zai Shafa Ya Gane.


Romeo matashi ne wanda ya rasa idanun sa a yayin da yake shekaru biyu da haihuwa, amma hakan bai hana shi cimma burin sa na rayuwa ba, kuma ya yi karatunsa ne a fannin jarida.

Matashin yana amfani da amo ko sauti wajan saurarren kwallon kafa domin shi ma’abocin kwallon kafa ne, kuma ya bayyana kansa a matsayin ma’abocin wasu nau’ukan abinci wadanda ya ce yake ganewa ta wajan dandanon su.

Wani abu guda shine gane yadda yanayin zane zane suke a birnin New York. Romeo ya ce ya tuna wata rana da kakarsa ta kai shi yawon shakatawa a wani gidan tarihi dake birnin New York, inda ya kai hannunsa a bango ya sai kawai ya ture wani hoto da aka makale a bango.

Matashin ya kara da cewa masu gadin wurin suka yo masu ca!, sai kakar sa ta basu hakuri sa’an nan ta bayyana masu cewa yana da matsalar gani.

Wani tsohon mai daukar hoto a mujallar sha’anin rayuwa ta Live Magazine John Olson, ya gano wata hanya ta Amfani da fasahar bayyana hotuna ta surori uku da makafi zasu shafa kuma su gane suffer hoton.

Olson, ya bayyana cewa watarana tunanin yadda makafi ke gane surar abu ya fado masa a rai, sai ya fara tunanin yadda zai kirkiro da sabuwar fasahar yin hakan. Da farko yakan yi fent aka fatar wanda zai fitar da zane mai surori uku, daga nan sai a turawa kwamfutar da zata siffanta shi.

Daga nan sai ainihi siffar da ake bukata ta bayyana, kuma dukkan ayyukan kan dauki har tsawon makonni hudu. Wannan yakan ba makafi damar gane dai dai yadda siffar hoton take da zarar sun sa hannu sun shafa shi.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG