Sakamakon wani bincike ya bayyanar da Karnuka a matsayin masoya mutane, kana dabbobi da su kafi saurin fahimta. Binciken da aka gudanar a kasar Hungary, ya tabbatar da cewar, karnuka suna fahimtar maganar iyayen gidan su, kamar mutane da kuma kokarin aiki da umurni yadda ya kamata.
A wani daukar hoton kwakwalwar karnuka, da akayi wanda ya bayyanar da cewar, gefen kwakwalwar kare na hagu, ya kanyi aikin tunani a lokacin da kare, yake sauraren magana. Haka bangare dama kuwa, ya kanyi tunani don aiwatar da abun da aka umurce shi da yayi.
Kusan binciken ya bayyanar da cewar babu wani banbanci mai yawa, tsakanin yadda mutun ke tunani da kare, duk kwakwalwar na aiki iri daya. A lokacin da aka saka karnuka da akayi gwajin a kansu, cikin kwamfuta don duba kwakwalwar su, basu yi wani abu da ya banbanta su da mutane ba.
A lokacin binciken an gwada yadda karnukan suke, daukar magana da amfani, da abun da aka umurce su, wanda duk binciken ya kara tabbatar da cewar, sune dabbobi da su kafi kusanci da mutane, kana da shakuwa mai nagarta a tsakanin mutun da dabba.