Mark ya furta hakan ne a lokacin wata ziyarar bazata da yake birnin Legas, a Najeriya, domin gaawa da matasa da ‘yan kasuwa masu hazakar kirkire kirkiren na’urori na fasahar zamani daban daban.
A lokacin wannan ziyara dai Zuckerberg, ya gana da masu kirkire kirkire a cibiyar bunkasa dabarun zamani ta C.C Hope da ke birnin Legas. Usman Ibrahim Usman, daya daga cikin matasa masu fasahar kirkirar man hajar yanar gizo daga Arewa bayyana alfanun wannan ziyarar ta matashin biloniyan ga masu ilimin fasahar yankin Arewaci n kasar.
Yace makasudin zuwansa shine domin a kara bunkasa kafofin bayanai na Najeriya, saboda irin ci gaban da kasar ke samu da kuma ilimin kimiyya na wasu abubuwa da Najeriya ke da shi, da kuma kara bude hanyar ci gaba.
Wannan ziyarar dai ita ce karon farko da mai shafin Facebook matashi Mark Zuckerberg ya kai wata kasa a Nahiyar Afirka.