A cikin shekarar 2014, ne Mr. Joseph da matar shi Danielle, suka shirya tafiya hutu, zuwa garin da aka tabbatar da cewar shine gari, da yafi kowanne gari wajajen shakatawa musamman ga yara. Tafiyar da su kayi daga garin “San Leandro zuwa Disneyland” a jihar Florida, ta kasar Amurka.
Ta kai kimanin tafiyar kilomita dari biyar da saba’in 570, kimanin tafiya daga Abuja zuwa Zamfara. Bayan sun isa sai suka sauka a hotel mai suna “Grand Californian Hotel” wanda yake daya daga cikin manyan otel a garin.
Wayewar gari ke da wuya, sai ‘yar su mai shekaru tara da haihuwa, ta sanar da iyayen cewar, bata samu bacci ba cikin dare, domin kuwa wani abu ya cije ta. Daga bisani koda iyayen suka duba sai suka ga cewar ashe kudin cizo ne ya addabi yarinyar.
Shekaru biyu kenan da abun ya faru, sai ga Mr. Joseph, ya shigar da otel din kara a gaban kotu, da cewar otel din basu kyautata musu ba, wanda sanadiyar rashin yin aikin su yadda ya kamata ‘yar su ta kamu da rashin lafiya, biyo bayan cizon kudin cizo a dakin su.
Sai suka kara da cewar, yana da kyau mutane su san wane irin otel zasu dinga sauka, don kare lafiyar su da ta iyalan su. Haka suma gidajen kwana su kokarta wajen inganta sana’ar su. Yanzu dai za’a cigaba da shari’a.