Fathia Ayodele Kareem, ‘yar Najeriya, mai shekaru ashirin da biyar da haihuwa 25, ta kafa tarihi a jami’ar “Kwame Nkrumah” dake kasar Ghana, inda ta kammala karatun likitanci, kuma ta lashe kyaututuka goma sha biyu 12, cikin kyaututuka goma sha biyar 15, da aka bada.
Matashiyar likitar Fathia, ta kafa babban tarihi, wanda tun bayan kafa makarantar shekaru arba’in da daya 41, da suka wuce, ba’a taba samun wanda yayi irin abun da tayi ba. An bata wadannan kyaututukan ne a ranar rantsar da su a matsayin likitoci, masu cin gashin kansu.
Ta bayyanar da babban burin ta, shine ta zama kwararriyar likitan yara, a nan gaba. A lokacin da aka tambaye ta, ta kuwa yi tunanin samun wadannan kyaututukan?, sai tace, lallai ta san da cewar zata samu wadannan kyaututukan, dalili kuwa shine, domin tayi karatu matukar gaske.
A karshe ta bayyanar da dalilin da ya kaita ga wannan nasarar, da cewar irin gudunmawa da ta samu daga iyayen ta, abokai, da ‘yan’uwa da abokan arziki. Haka kuma ta nace matuta wajen karatu, ba dare ba rana. Haka kuma idan matasa za suyi hakan, babu abun da zai sa ba suyi nasara a komai suka sa a gaban su.