RIO 2016: 'Yan-Wasan Najeriya Za'a Cigaba Da Damawa Da Su!

Wasan Rio 2016

Burin kowane dan wasa shine, kada a tashi wasa bashi da wata nasara da zai nuna ya samu. ‘Yan wasan kwallon kafar Najeriya, sunyi rawar gani a wasannin Rio 2016, inda suka lashe babbar kyautar Azurfa.

‘Yan wasan sun buga wasan su na karshe, da ‘yan wasan kasar Hondura, inda aka tashi da ci 3 – 2, a ranar Lahadi da ta gabata. Nasarar dai ta samu ne a yayin da dan wasa Aminu Umar, ya saka kwallo daya a raga tsakanin mintoci 34 zuwa 49.

Inda shi kuma Sadiq Umar, ya saka kwallo da ta bama ‘yan Najeriya, damar samun maki 3 da babu, a kan abokan karawar su na kasar Honduras. Wannan kyautar dai itace kyautar babbar Azurfa, da duk ‘yan wasan Najeriya suka lashe a cikin duk gasar ta Rio 2016.

Azurfar karshe da ‘yan Najeriya suka taba samu a yayin wasan, ‘yan matan Najeriya, a shekarar 2008. Hakan dai yasa yanzu kasar ta lashe jimillar Azurfa ashirin da hudu 24. Kasar nada kalar Azurfa Gold na shekarar 1996, sai Silver a shekarar 2008, yanzu kuma Bronze a sheakarar 2016.