Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Yiwa 'Yar Flying Eagles Sama Da Fadi Da Kudadansu


Kungiyar kwallon kafa ta Flying Eagles wadanda suka wakilci Najeriya, a gasar Olympics, da ake gudanarwa Rio De Janeiro, ta kasar Brazil sun doke Honduras, da kwallaye ukku da biyu.

Wannan nasara da kungiyar kwallon Najeriya, ta samu, ya bada damar lashe mataki na ukku, wanda ya bata damar samun tagula.

A wata sabuwa kuma akwai wata ‘yar takaddamar da ta taso tsakanin ‘yar wasan da hukumar kwallon kafa ta Najeriya, akan wasu kudade da wani Likita dan kasar Japan, mai suna Katsuya Takasu, ya yiwa ‘yar wasan alkawari dalar Amurka, $390,000.

Shi dai Likita Katsuya Takasu, wanda ya kasance masoyi ‘yan kwallon Najeriya, ya yi wannan alkawari ne ganin irin tsaka mai wuyar da ‘yar wasan suka fuskanta a wasani da suka shafi harkar kudi ne.

Ana zargin cewa hukumar na neman yi sama da fadi da kudaden, abinda shugaban hukumar Amaju Pinnick, ya musanta yana mai cewa ana son kudaden su bi hanyar da ta dace ne kasancewar Najeriya ‘yantatciyar kasa ce.

XS
SM
MD
LG