Divine Ejowvokoghene Oduduru, dan tseren Najeriya, ya zamo na biyu a cikin wasan da ake gabatarwa na Rio Olympics 2016. Divine ya biyo bayan shahararren dan tseren kasar Jamaica, Usain Bolt. Hakan dai ya saka shi a cikin jerin ‘yan tsere da zasu shiga gasar a zagayen kusa da karshe.
Dan tseren dai yanzu ya karrama kasar Najeriya, damar samun zinariya, a inda ya zamo na biyu, yanzu zai fuskanci wani babban kalubale na gudun mitoci dari biyu 200M.
Shi dai dan wasan mai shekaru goma sha tara 19, ya samu wannan nasarar ne a lokacin da ya isa kan layi, cikin mintoci ashirin da dakika talatin da hudu 20.34, inda shi kuwa Usain Bolt ya kai karshe a cikin minti ashirin da dakika ashirin da takwas 20.28.
Dan tseren dai ya dau alwashin ganin ya lashe babbar kyautar, a wasan da zasu sake zubawa. Ya dai kara da cewar, yasan wannan ba wai abu ne mai sauki ba, kasancewar dan wasan kasar Jamaica, na ciki, amma yana da karfin tabbacin cewar zai yi nasara a gasar karshe.