Wani tsohon dan wasan Olympic da ya taba wakiltar Ghana a wasannin Olympic na shekarar 1984 Reks Brobbey, yace zai iya farfado da wasannin guje guje da ya tabarbare.
Tsohon dan wasan ya ce a cikin shekaru bakwai daga yanzu tare da taimakon kampanoni zai miya cimma wannan buri na farfado da wasan guje guje a kasar Ghana, ta yadda kasar zata yi abin bajinta a wurin wasani.
Brobbey ya bayyana sha’awarsa ga wannan wasannin shekaru hudu da suka wuce lokacin da ya fito da wani shirin gasar wanda yafi saurin gudu a Ghana wanda ya samar da 'yan wasannin guje guje guda biyu da suke wakilci Ghana a wasan Olympic da ake yi a halin yanzu.
Ya kara da cewa ba sai mutum ya zama shugaba hukumar Olympic sa’annan zai iya horar da yan wasa ba. Yace kowa nada baiwar da Allah yayi mashi kuma nasa bawar ce ya habbaka wasannin guje guje kuma bashi da sha’awar zama shugaba kungiyar 'yan wasan guje guje ta Ghana.