Oluwatunmise Idowu, yarinya mai shekaru goma sha uku 13, ta kafa tarihi, inda ta amsa tambayoyi goma sha bakwai 17, na lissafi cikin minti daya. Yarinyar ‘yar aji uku 3, na makarantar sakandire “JSS 3” tayi abun da a tarihin gasar cikin kyautar masu hazaka, na kamfanin “Promasidor Nigeria Limited” ke shiryawa duk shekara.
Akan dai zakulo yara matasa don basu damar shiga wannan gasar, inda ake basu wasu matsaloli na lissafi su fitar da amsar cikin kankanin lokaci, ita dai wannan yarinyar ta amsa tambayoyin goma sha bakwai cikin kasa da minti daya. Hakan yasa ta lashe gasar inda aka bata kyautar naira milliyan daya.
A lokacin da manema labarai suke ganawa da yarinyar, ta danganta nasarar ta da irin naci da take da shi wajen karatu, da kuma yadda take ware kimanin awowi hudu 4, a kullun don warware wasu matsaloli na lissafi.
Ta kuma bayyanar da cewar, duk wasu matashi zasu iya samun irin wannan nasarar, idan har suka sama kansu, musamman idan suna yawan karatu. Tana kara godiya ga Allah, da iyayen ta, haka da malamanta sai abokanta da suke bata kwarin gwiwa, har ta kaiga wannan matakin.