Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wake Son Ganawa Da Shugaban Kasar Amurka Barack Obama?


Shugaba Barack Obama.
Shugaba Barack Obama.

A karon farko a tarihin duniya, fadar shugaban kasar Amurka “White House” sun kirkiri wata dama, da ‘yan kasar zasu iya ganawa da shugaban kasar kai tsaye.

A wata sanarwa da ofishin ya fitar da cewar, kamar yadda mutane ke ganawa da abokan su ta shafin zumunta na facebook, suma yanzu haka sun kirkiri wata dama kamar hakan.

Mutane zasu iya amfani da, damar aika sako na “Facebook Messenger Bot” don aika sakon gaggawa ga shugaba Barack Obama, wannan hanyar bama ‘yan kasar damar fadan albarkacin bakin su ne ga shugaban kasa kai tsaye.

Mutane kimani sama da 1,880 kan rubuta ma shugaban kasar wasika, akai-akai wanda yake karantawa a koda yaushe, yanzu haka wannan wata damace da zasu yi magana batare da shamaki ba.

Tun bayan tsarin tsohon shugaban kasar Abraham Lincoln, na fitowa waje don ganawa da jama’ar kasar, sai a wannan karon aka sake samun wata dama makamanciyar haka, da shugaban kasa zai gana da mutanen shi kai tsaye.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG