Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan-Matan Zamani Ga Maganin A Cuci Maza "Gashi"!


Gashin Kai!
Gashin Kai!

Taron masana binciken lafiyar gashi da fatar jikin dan’adam, sun bayyanar da wasu abubuwa da kan iya zama hadari ga lafiyar gashin mutun, musamman ‘yan mata. Anabel Kingsley, likitan gashi da fatar kai, a tsangayar Philip Kingsley. Tayi bayani akan nau’o’In gashi da yadda ya kamata mutane su dinga kula da gashi.

Ta fara da cewar, akwai man wanke gashi kala daban-daban, wadanda suke dauke da sinadarai iri-iri, a wasu lokutta man da ya karbi wata, yana iya zama lahani ga wata, hakan na nuni da cewar, kowace mace nada bukatar ta duba wane irin mai ne yayi dai-dai da irin gashin ta. Haka matasa su sani kusan kowace hallita da irin yanayin gashin su, musamman mutanen yankin kasashen Asiya, da kasashen Turai, haka da mutane kasashen Afrika, da kasashen larabawa, kowane da irin gashin su.

Da yawa mutanen wasu yanki idan sukayi amfani da wani mai da yake kara lafiya a gashi na mutanen wani yanki, su yakan iya zama lahani gare su. Musamman mutane da suke yanki Afrika, da Asiya, suna da karancin, da karfin gashi, don haka yana da kyau su dinga neman irin man da zai dace da kansu kamin suyi amfani da shi.

Kada mata su dinga wanke gashi cikin sauri, babu wani tattali, ko su dinga wanke gashi a koda yaushe, idan da hali su dinga shafa mai da ya kamata da wanke gashin akai-akai. Kada su dinga shafa mai a busashen gashi, don ba zai dinga kaiwa ga gashin ba, a karshe zai zauna a saman gashin ya kuma zama matattarar datti.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG