Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aicha Macky: Babu Sana'ar Da Macce Bazata Iyaba, Idan Tana Da Ilimi!


Aicha MACKY
Aicha MACKY

Aicha Macky, tayi rubuce-rubuce, da jagorantar shirya fina-finai, don kara wayar da kan mutane, da suke karkara a duk cikin ilahirin kasar Nijar. Daya daga cikin fim dinta da yayi fice shine "Arbre Sans Fruit" da ya fito a watan mayu 2016.

Fim din ya samu karbar lambar yabo na "Africa Movie Academy Awards" a babban birnin Patakol, kasar Nijeriya inda ya ci kyauta ta farko na fim mafi tasiri na kasashen Afrika a shekarar 2016.

Aicha, tana jan hankalin mata ma su yin fina-finai da su bada kaimi wajen neman ilimi mai zirfi, dan ganin cewa sun habaka wannan sana'ar da muta ne da dama suke ganin cewa maza kadai ke iya yin aikin.

Kuma tana kira da mazaje, da su zamanto masu bada hadin kai, ga mata dan ganin sun cinma burin su nayin aikin da ransu ya keso, ba tare da sun saba ma addini, ko al'adun su ba.

Aicha, na daya daga cikin bakin shugaban kasar Amurka Barack Obama, na shirin YALI, inda ta kammala karatu na fannin jagorancin jama'a a jami'ar Wagner College a jahar New York.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG