Gwamnatin jihar Kano ta ce , ta tura wasu matasa 100 zuwa kamfanin hada motoci ta ‘Peugeot’ da ke Kaduna don zama masu dogaro da kan su, a yunkurin taimakawa matasa.
Kwamishinan yada labarai harkokin cikin gida matasa da al’adu na jihar Kano, Mohammad Garba ya bayyana haka a wata tattaunawa da wakiliyar Dandalinvoa, Baraka Bashir, a bikin ranar matasa ta duniya.
Hukumar asusun kula da yawan jama’a na majalisar dinkin duniya ta ce rashin aikin yi ga matasa ya kai kololuwar gaske a duniya baki-daya, kuma samar mu su da damarmaki da kuma tattauna wa tare da su na daga cikin makasudin taken bikin ranar na bana.
Taken bikin ranar matasa ta duniya na bana dai shine, Kawar da Fatara tare da samar da dorarriyar hanya a bangaren ciyar da al’umma abinci kafin nan da shekarar 2030.
Domin haka ne majalisar dinkin duniya tayi harsashen cewa da matasa zasu gudanar da aiyukan tallafawa al’umominsu zai taimaka wajan ci gaban kasasshen su tare da samarda zaman lafiya a duniya.