Muhibbat: Daya Daga Cikin Mata 'Yan Najeriya Masu Juya Tattalin Arzikin Duniya!

Muhibbata Abdullahi,

Muhibbat Abdullahi, yar asalin jihar Bauchi ce, a Arewacin Nijeriya. An haife ta a cikin garin Bauchi, inda tayi makarantan firamare a makarantar Bakari Dukku da kuma karatun sakandire a makarantar Mata ta Bauchi “Government Girls College, Bauchi” Tayi nasaran cin jarabawar shiga Jami'a “JAMB” inda tasamu daman shiga jami'ar Abubakar Tafawa Balewa dake garin Bauchi a 2009, inda ta kammala karatun ta da sakamako mai daraja ta biyu “second class division” a shekara ta 2015 a Fannin tattali da adana “BSc Accounting.”

Yayin karatun ta a Jami'a ta samu tallafin karatu (scholarship) na dalibai masu kwazo da hazaqa daga kamfanin man fetur na 'Total-Elf' da kuma kungiyar mata akauntoti na Nijeriya “Society for Woman Accountants in Nigeria” (SWAN) inda suka dauki nauyin karatun ta har gamawa.

Muhibbat, matashiya ce mai son karatu da dogaro da kanta, inda ta fara harkan dogaro da kai, da kasuwanchi tun tana Jami'a da dan karamin Jari, inda daga baya a shekara ta 2013, ta samu tallafi daga gwamnatin tarraya a shirin gwamnati na YouWIN, don bunkasa harkokin kasuwancin ta. Muhibbat itace makirkira kuma shugaban kamfanin nan na “Muhibbaty Global Enterprises.”

Muhibbat tana ganin mata da matasa, da su nemi ilimi mai zurfi, kuma su zama masu dogaro da kansu, don cigaban kasa domin gwamnati ba zata iya samar wa kowa aiki ba. Ta hakan zasu zama masu taimaka wa gwamnati wajen kirkiran aiki ba masu neman aikin da babu ba.

Mazaje ma da iyaye su bar matansu da 'yayan su mata, su karo ilimi kuma su barsu su nemi na kansu don cigaban al'umma da bada ilimi mai amfani wa yara masu tasowa domin ilimantar da yaya mata ilimantar da al'umma ne.

Muhibbat, na daya daga cikin bakin shugaban kasar Amurka Barack Obama, daga kasashen Afrika. Yanzu haka tana jami'ar “Purdue” dake garin Indiana don nazari da samun horaswa a fanin kasuwanci.