A duk lokacin da matasa suke kokarin shiga cikin rayuwar soyayya, to kada su manta da wasu abubuwa guda biyar 5, wadanda zasu taimaka musu wajen zaben mace da ta dace da su. Wasu masana halayyan dan a’dam sun bayyanar da wasu abubuwa biyar da, duk na miji ko mace suka dauke su, babu shakka baza suyi kunya ba.
Kamin ka zurfafa cikin kogin soyayya da mace, yana da kyau kasan wane irin tarbiyya iyayen ta suka bata, musanman mahaifi, irin ‘yayan nan ne da ake shagwabawa? Ko kuwa irin yaran da basu da kamun kai ne suna iya tanbayar saurayi wani abu?
A duk lokacin da kake kokarin kiran mace amma tana yawan yimaka kukan cewar ta gaji, koda kuwa bata yi wani aiki da ya kamata ace ta gaji ba, ko kuma ka fuskanci cewar bata son duk wani aikin motsa jiki, ta cika son kanta. To kaji tsoron irin su.
Macece mai tausayi ko kuwa irin zubin matane da basu da damuwar halin da mutun ya shiga. A wasu lokaci yana da kyau ka gwada ta da wani abu don ganin yadda zata dubi abun, idan ta nuna tausayi da damuwa to lallai sai ka kara gyara dangantar ku.
Hakama duk mace da ka lura tana da alamun rashin gaskiaya a tare da ita, dangane da tarayyar ku, to itama ba mace da ta dace mutun ya nema bace. Gaskiya da mutunta juna shine babban ginshiki a duk rayuwar wasu masoya.
A karshe kuwa, yana da kyau mutun ya duba irin yadda mace take nuna kauna da damuwa ga ‘yan’uwan ka da abokan ka. Haka yana da kyau mutun ya duba yadda mu’amalarta take da wane irin kawaye gare ta. A duk lokacin da mutu ya samu mace da ta dauki wasu daga cikin hallayan nan na kirki, to sai mutun ya bada azama, samun akasin haka kuwa, yana bama mutun kwarin gwiwar neman mafita.