Dan Wasa "Lionel Messi" Yayi Sabon Gyaran Kai Don Bada Tsoro!

Dan wasa Lionel Messi

Shahararren dan wasan kwallon kafar duniya “Lionel Messi” na kungiyar kwallon kafar Barcelona. Ya bayyanar da irin shirin da ya keyi don tunkarar kakar wasa mai zuwa. A jiya ne, budurwar shi kuma maman ‘ya’yan shi biyu, Antonela Roccuzzo, ta saka hoton shi a shafin zumunta na “Instagram”

Dan wasan Messi, ya sake kalan gashin shi daga baki zuwa fari, wanda yake nuna cewar, a wannan kakar babu abun da zai sa suyi kasa a gwiwa. Ganin cewar ya rasa saka kwallo a raga, a yayin da suka samu damar buga kwallon daga kai sai mai tsaron gida, a wasan su da Copa America.

Kuma ya bayyanar da jin dadin shi da zuwan ‘yan wasa kamar su Aaron Ramsey, da Samir Nasri, haka da Phil Jones, cikin kungiyar. Wadanda yake sa ran zasu hada karfi da karfe, wajen ganin sun samar da klob da zai kafa tarihi a fadin duniya kwallon kafa.