Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Kula Da Harkokin Wasannin Olympic Ya Dakatar Da Hukuncin Hana 'Yan Kasar Rasha Wasa


Kwamitin dake kula da harkokin wasannin Olympic IOC a takaice, ya yanke shawarar barin duk ‘yan wasan kasar Rasha su yi wasa a gasar Olympic da za a fara wata mai zuwa a Rio, saboda zargin kasar da amfani da kwayoyi masu ‘kara kuzari.

A lokacin da yake magana a jiya Lahadi, shugaban kwamitin IOC Thomas Bach, ya ce kwamitin ya dakatar da hukuncin dakatar da kasar a wasannin saboda kare ‘yancin ‘yan wasan da basu yi amfani da haramtattun kwayoyin ba don samun kuzari kan abokan karawarsu.

Mr. Bach yace za a iya cewa wannan abu ne da kungiya ta aikata, kuma za'a iya korar kowa, amma daga karshe dole a kalli idon kowane ‘dan wasa a yi tunanin hukuncin da aka dauka.

Amma kuma kwamitin IOC ya bayyana cewa dole ne a saka ido kan gwajin da za a yi wa ‘yan wasan Rasha a wasanni 28 da za ayi wanda za a fara ranar 5 ga watan Agusta a Rio de Janeiro.

A jiya Lahadi a birnin Moscow, Ministan wasanni Vitaly Mutko ya bayyana jin dadinsa da kwamitin IOC bai ‘dauki matakin hana ‘yan wasan Rasha baki ‘daya yin wasa ba, bayan da Hukumar Yaki Da Shan Kwayoyin Kara Kuzari ta Duniya WADA ta zartas da hukuncin a makon da ya gabata.

A rahotan da hukumar WADA ta fitar na makon da ya gabata na cewa sama da ‘yan wasa 30 ne gwamnati ta samar musu kwayoyi masu ‘kara kuzari.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG