Yawaita Amfani Da Shafukan Zumunta Na Yanar Gizo Na Shafar Ilimin Matasa

Bincike ya nuna cewa lokacin da matasa ke kashewa wajan amfani da shafukan sada zumunta na yanar gizo da aka sani da suna social media a turance, na kara yawa. A halin da ake ciki yanzu na wannan karni na 21, idan mutum baya mu’amula da wadannan shafuka tamkar yana zama cikin yanayin lokutan da suka gabata ne, wato mutum bai waye ba Kenan.

Amma abin tambaya anan shine, ka taba tunanin daina amfani da wadannan kafafen sada zumunta na social media irin su facebook, da twitter, da Instagram, zuwa irin su snapchat da sauran su?.

Yawancin matasa na bata lokaci mai tsawo akan wadannan shafuka a maimakon yin amfani da wadannan lokuta wajan karatun litattafai, ko zantawa da ‘yan uwa, ko kuma gudanar da harkokin kasuwanci.

Yawaita amfani da shafukan social media kamar yadda aka wallafa a shafin mujallar vanguard, na daya daga cikin dalilan da suka haddasa yawan faduwa jarabawa da matasa ke yi, kuma idan ba’a shawo kan lamarin ba, lallai za’a sami komabaya a harkokin ilimi dama cigaba a fannin kimiyya da fasaha, da kirkire kirkire da sauran su.

Matasa na iya sauya tunanin su musamman wajan daina bata lokacin su wajan hira da abokai ko musayar hotuna ta wajan mayar da hakali akan karanta litattafai ko gudanar da wasu muhimman ayyukan da zasu mora a rayuwa kuma tabbas zasu ga alfanun hakan.