Allah Kadai Zai Kwaci Kungiyar Super Eagles -Inji Tijjani Babangida

Tsohon shahararren dan wasan kwallon kafar nan na Najeriya Tijjani Babangida ya yanke hukunci akan shirye shiryen da kungiyar kwallon kafa ta Najeriya ke yi na zuwa gasar wasannin cin kofin duniya na shekarar 2018, cewa sai dai wani iko daga Allah ne kadai zai kwaci kungiyar Super Eagles a kasar Rasha.

Tijjani Babangida ya bayyana cewa sai dai ikon Allah ne kadai zai kwaci kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles a wasannin kwalon kafa da za a buga Rasha domin a cewarsa, kungiyar Super Eagles bata yi shirin da har zata iya karawa da kungiyoyin da kasar ta sami kanata a cikin rukunin su ba.

Tsohon shahararren dan wasan ya bugawa Najeriya wasa a wasannin cin kofin duniya na shekarar 1998, kiuma ya rike mukamin mataimakin babban kocin kungiyar Super Eagles a karkashin tsohon kocin kungiyar Sunday Oliseh.

Tsohon dan wasan ya kara da cewa a lokacin da sauran kungiyoyin kafa ke fama da motsa jiki da shirye shiyen gasar wasannin da za’a fara a watan Oktoba mai zuwa, kungiyar Super Eagles ko dauwamammen Koci basu da shi.

Ya ce “haka ta faru a lokuta da dama, gashi kuma a wannan karon muna rukuni guda da kungiyar kwallon kafa ta kasar Kamaru, da Zambiya, da kuma Algeriya, Allah kadai zai kwaci kungiyar Super Eagles daga wannan rukunin.”

“a maganar gaskiya mun san cewa wasan kwallon kafa babu yadda baya iya kasancewa amma gaskiya sauran kasashen na iaya tabbatar maka da cewa a shirye suke dari bisa dari, amma kungiyar Super Eagles bata ma san wanene babban kocin ta ba”.

Your browser doesn’t support HTML5

Allah Kadai Zai Kwaci Kungiyar Super Eagles -Inji Tijjani Babangida