A wasan kwata-fainal na gasar Copa America, Chile ta ba kowa mamaki a lokacin da ta doke kasar Mesxico da ci 7 da babu, Ga jerin hotuna daga wannan wasa na tarihi
Chile Ta Yi ma Mexico Dukar Da Ba A Taba Yi Mata Ba: Ci 7 Da 0 A Gasar Copa America
A wasan kwata-fainal na gasar Copa America, Chile ta ba kowa mamaki a lokacin da ta doke kasar Mesxico da ci 7 da babu, Ga jerin hotuna daga wannan wasa na tarihi

1
'Yan wasan Chile sun hadu su na murna a bayan da Edson Puch ya jefa kwallo a ragar 'yan Mexico a wasan kwata fainal da suka buga na gasar Copa America a filin wasa na Levi's Stadium dake Santa Clara, a Jihar California

2
Dan wasan Chile, Edson Puch (hagu) da dan wasan Mexico Andres Guardado su na neman kwallo a karawar ta su.

3
Dan wasan Mexico, Javier Hernandez, na biyu daga hagu da Arturo Vidal na kasar Chile (mai sanye da riga mai lamba 8) su na kokawar neman kwallo a lokacin karawar tasu.

5
Edson Puch na Chile da sauran 'yan wasan kasarsa su na murnar jefa kwallo a raga.