Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FIFA Ta Sanar Da Kasashen Da Najeriya Zata Gwabza Dasu A Gaban 2018!


Hukumar FIFA
Hukumar FIFA

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta ayyanar da kungiyoyin da ‘yan wasan Najeriya, “Super Eagle” zasu fuskanta a wasannin zakaru na shiga gasar cin kofin duniya a shekarar 2018.

Kwamitin kungiyar ya gudanar da wannan zazzafar tattauanawar ne a shelkwatar ta kasar Egypt, a yayinda aka hada kasar Cameroon, Algeria, da Najeriya a rukunin B, sai rukunin C, da ya hada da kasar Cote d’ivoire, Morocco. ‘Yan waje kuwa sune kasar Libya, da Burkina Faso, suma kasar Tunisia, da Senegal suna ciki.

Wannan shine mataki mai matukar wahala da kasashen Afrika, suke ciki don neman gurbi a gasar cin kofin duniya. Tun a watan Oktoba da ta gabata aka fara da kasashe ashirin 20, wanda zasu kara da junan su a gida da waje, za’a fara da rukunai guda biyar, wanda idan suka samu nasara zasu shiga cikin ‘yan wasan da zasu je gasar a kasar Russia 2018 kai tsaye.

Za dai a kwashe watannin goma sha biyu ana wasan, wanda za a fara a watan Oktoban 2016 zuwa Nuwambar 2017. Rukunin A: Libya (2), Guinea (4), DR Congo (3), Tunisia (1) Rukunin B: Zambia (1), Cameroon (2), Nigeria (4), Algeria (3) Rukunin C: Gabon (1), Morocco (4), Mali (2), Cote d’Ivoire (3) Rukunin p D: Burkina Faso (3), South Africa (2), Cape Verde (4), Senegal (1) Rukunin E: Uganda (4), Congo (3), Egypt (2), Ghana (1)

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG