Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Kaftin Joseph Yobo, Zai Koma Buga Wasan Gida!


Tsohon dan wasan Nijeriya Joseph Yobo.
Tsohon dan wasan Nijeriya Joseph Yobo.

Tsohon kaftin na kungiyar kwallon kafar Najeriya, “Super Eagle” Joseph Yobo, ya bayyanar da cewar zai koma bugama kungiyoyin gida wasa. Dan wasan ya bayyanar da hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai.

Yace dalilin shi na komawa shine, don yana da sha’awar ganin ya taimakama kasar shi, domin ita ta kaishi inda yake yanzu. Yana ganin abun da yafi dacewa da shi, shine ya dawo don koyar da yara masu tasowa sana’ar kwallo da yadda zasu iya zama zakaru a manyan klob na duniya.

Yanzu haka dai, tsohon dan wasan ya cinma matsaya da kungiyar zakarun ‘yan wasa ta Najeriya, wanda yake sa ran zai buga wasa goma sha biyu masu zuwa. Har ya zuwa yanzu bai bayyanar da klob din da zai koma ba, amma dai ana sa ran tsakanin klob din Kano Pillars, Akwa United, IfeanyiUbah FC ko Willi Tourist, cikin su zai koma kungiya daya.

A tabakin mai magana da yawun dan wasan, yace shi Yobo, bawai yanason dawowa kungiyar ta gida bane, don ya samu kudi. A’a yana son dawo wane don shima ya bada tashi gudun mawa wajen ciyar da kasar gaba, domin kuwa duk kudin da ake nema ya same su a rayuwa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG