Ya Rasu Ya Bar Ni Da 'Ya'Ya Goma - Inji Wata Mata A Ranar Tunawa Da Matan Da Suka Rasa Mazan Su Ta Majalisar Dinkin Duniya

Yau ce ranar da majalisar dinkin duniya ta ware domin tunawa da matan da suka rasa mazajensu a fadin duniya, irin wannan rana nada matukar muhimmanci kwarai da gaske musammam ga irin wadannan mata da mazan su suka rasu suka bar masu kananan yara wadanda yawanci suka fada cikin halin kunci domin rashin masu daukar nauyinsu.

Wadannan mata da kananan yara musamman a nahiyar Afirka da kuma arewacin Najeriya inda kungiyar boko haram ta hallaka jama’a da dama na mayukar bukatar taimako.

A arewacin Najeriya, irin wadannan mata da suka rasa mazansu na fuskantar matsalolin rayuwa domin kuwa yawancin yaran da mazan da suka rasu suka bar masu na kasancewa kara zube, babu abinci, ba makaranta, hatta ma matsuginin da zasu zauna babu.

A hirar da wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka Haruna Dauda Biu yayi da wasu daga cikin matan da suka sami kansu cikin wannan hali a sakamakon rigingimun kungiyar Boko haram, sun bayyana irin halin da suke ciki.

A cewar wasu daga ciki, na farko dai babbar matsalar da suke fuskanta ita ce rashin abinci, da rashin lafiya, sai kuma rashin inda zasu sa kansu domin basa iya biyan kudaden hayar gidajen da suke zama, haka kuma yaran da aka barmasu basa samun damar halartar makarantu.

Wasu daga cikin matan da wakilin ya sami ganawa dasu nada ‘ya’ya goma, wasu kuma takwas wasu biyar da sauran su, kuma duka sun bayyana cewa sun rasa mazan nasu ne a yayin da ‘ya’yan kungiyar Boko haram suka kai masu hari.

Saurari Cikakken Rahoton.

Your browser doesn’t support HTML5

Ya Rasu Ya Bar Ni Da 'Ya'Ya Goma - Inji Wata Mata A Ranar Tunawa Da Matan Da Suka Rasa Mazan Su Ta Majalisar Dinkin Duniya