Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rabon Mutun Baya Wuce Shi, Ko Ana Mazuru Ko Ana Shaho!


Tagullar Zinariya.
Tagullar Zinariya.

Masu iya magana dai kance “Abincin wani gubar wani” Mr. Joe Jacob, dan wasan Olympics ne, wanda ya samu nasarar samun kyautar tagular zinare a shekarar 1992. A makonnin da suka gabata, yana cikin tafiya zuwa wani gari.

Ya tsaya don cin abinci, wasu bata gari suka bude motar shi, suka sace mishi kaya. Amma abun Allah, bai basu damar ganin wannan tagullar ba. Sun duba cikin jakar shi da suka sace, amma basu ga komai ba sai kayan sawa da suka yar dasu cikin bola, don haushin bashi da wani abun so.

Mr. Wayne Smith da ‘yar shi Chlose, suna cikin binciken bola, sai yarinyar mai shekaru 6, da haihuwa taga wani abu, koda ta nunama baban ta sai sukaga tabullar zinariya ne. da sunan Mr. Joe, wanda suka tuntube shi a jihar Atlanta, ta kasar Amurka. Yayi bayanin cewar lallai da wadannan bata garin sunga wannan zinariyar, to da babu shakka ta halaka, amma saboda mutanen kirki ne suka gani, shiyasa ya sameta. Ya yima yarinyar mutumin kyautar girmamawa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG