Uwargidan gwamnan jihar Borno Nana Kashim Shettima ta yi kira ga attajiran jihar da su tallafawa marayun dake tangaririya akan titi wadanda suka rasa iyayen su a sakamakon rigingimun boko haram a arewacin kasar.
Uwargidan ta yi wannan kira ne a lokacin da take bada tallafin kayayyakin sallah da suka hada da shadduna ga wasu marayu a cikin garin Maiduguri, Uwargidan gwamnan ta ce ya zama wajibi su taimakawa wadannan marayu musamman akan harkokin da suka shafi harkokin iliminsu domin su zamo mutane na kwarai a rayuwa.
Ta kara da cewa wannan yanayi da suka sami kansu a ciki, basu ne suka yiwa kansu ba, Ubangiji ne ya dora masu, ta kuma roki wadannan marayu da su cigaba da yiwa wadanda suka rasa addu’a da kuma Najeriya baki daya domin samun zaman lafiya mai dorewa.
Marayu da dama sun bayyana irin halin kakanikayin da suke zama a halin yanzu, kuma sun mika gidiyar su ga Malama Nana Kashim Shettima data tuna dasu kuma har ta basu wannan taimako.
Saurari rahoton Haruna Dauda Biu Daga Maiduguri.
Your browser doesn’t support HTML5