Kama Manyan ‘Yan Boko Haram Ne Nasara Ko Ceto Garuruwa da Dazuzzuka

Sojojin Najeriya sun ceto wasu mutane a bayan da suka fatattaki 'yan Boko Haram daga wani sansaninsu dake dajin Sambisa a Jihar Borno

Sojojin Najeriya sun ceto wasu mutane a bayan da suka fatattaki 'yan Boko Haram daga wani sansaninsu dake dajin Sambisa a Jihar Borno

Babban abinda mutane ke son gani shine a kwana a tashi ba’a ji a kowane bangaren Najeriya jinin wadanda basu yiwa kowa laifi ya suba ba

Damke jigo a kungiyar Boko Haram, Albarnawy, ya zama abin alfahari ga jami’an tsaron Najeriya duk da a lokaci guda Boko haram, na fida wasu sakoni dake nuna sunanan kuma mubaiyar su na nan ga Abubakar Shekau.

Al-Barnawy, dai wanda akayi nasarar damke shi a jihar Kogi ya zaman abin farautar jami’an tsaron Najeriya da na Amurka.

Abdulrahaman Abu Hamisu, mai sharhi kan lamuran siyasa, yace wannan gagarumar nasara ce ga Gwamantin Najeriya, idan akayi la’akari da abinda ya faru can baya kullum ana koke koke na boma bomai da suke tashi, Sojojin Najeriya, ma kansu suna neman yadda zasu tsira da rayukan su wanda sau da dama suka gudu amma a can baya.

‘Yan gudun hijira ma yanzu sun fara komawa wanna ya nuna cewa an samu ci gaba fiye da abunda ake ciki can baya, har kuma ace an kama Albarnawy, yanu cewa akwai nasara a yakin da akeyi da ‘yan Boko Haram.

Akan batun shin Najeriya, ya dace ta hukunta Albarnawy, ko Amurka, masanin tsarin mulki, Barrister Luka Haruna, yace tunda a Najeriya aka kama shi kuma a nan yayi laifi sai dai kuma idan ya taba yin laifi a Amurka, ko awani bangare na duniya, wanda ake nemasa dokar Najeriya, ta bada dama ayi masa sharia a Najeriya, daga bisani a mika shi ga wata kasa.

Shin kama manyan ‘yan Boko Haram ne nasara ko ci gaba da amintar da garuruwa da dajijukan da ada ‘yan Boko Haram, suka yi Tunga ne nasarar, babban abinda mutane ke son gani shine a kwana a tashi ba’a ji a kowane bangaren Najeriya jinin wadanda basu yiwa kowa laifi ya suba ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Kama Manyan ‘Yan Boko Haram Ne Nasara Ko Ceto Garuruwa da Dazuzzuka -2'41"