Sojojin Amurka sun ce sun kwace wasu makaman da suka yi amannar daga kasar Farisa suka fito da nufin shigar da su hannun ‘yan Shi’ar Houthi da Iran din ke marawa baya a kasar Yamal. Wani jirgin sojan ruwan Amurka mai lakabin Sirocco ne da yake sintiri ya kama makaman a kan tekun Arabia ranar 28 ga watan jiya.
Makaman sun hada da bindigogi samfurin Kalashnikov guda 1500, sai makamin roka da ake harba bam daga nesa da su har guda 200, sai kuma manyan bindigogin masu sarrafa kansu kusan guda 50. Sojin Amurkan sun ce sun bar jirgin da ma’aikatansa sun tafi bayan karbe makaman.
Kwace makaman dai kusan karo na 3 kenan a cikin watanni 2 da aka kwace makaman da aka kudiri aniyar kaiwa ‘yan Houthi din, in aka hada da wadanda sojojin Australia da na Faransa suka kama a baya.
Kakakin Fadar White House Josh Ernest ya tabbatarwa manema labarai da lamarin kama makaman, inda shima Kakakin cibiyar tsaro ta Pentagon Peter Cook yace, wannan kamen ya nuna yadda Sojin Amurka ke aiki tukuru wajen sa idon tsaro a wasu sassan na duniya.