Makonni 2 bayan mummunar ,harin ta’addancin da aka kai a birnin Brussels na kasar Belgium, Shugaban Amurka Barack Obama da Babban Magatakardar rundunar tsaro ta hadin gwiwa ta NATO Jens Stoltenberg sun tambara wannan abu a matsayin wata masifa, tare da nuna bukatar tsayawa kai da fata akan yaki da ‘yan ta’addar ISIS.
A bayyane yake wannan lokaci duniya na fuskantar ta’adanci, sannan Turai na cikin ma’aunin da za’a maida hankali sosai wajen tsaurara matakan tsaro. Kamar yadda Obaman ya bayyanawa Magatakardar a cikin ofishinsa da ke fadar White House wanda aka yiwa lakabi Oval Office.
Shugaban kuma da yake magana da manema labarai bayan ganawar tasa da Stoltenberg, ya yabawa rundunar tsaron NATO game da kokarin da take yi a yaki da ta’addancin ‘yan ISIS, musamman hadin gwiwarta na horar da Sojojin kasashen Iraqi da Jordan.
Shima Mista Stoltenberg ya jaddada aniyar NATO akan tallafawa kasashen yankin don karfafa musu ,gwiwar yakar ‘yan ta’addar ISIS. Yace zasu yi aiki tukuru ne game da karfafa sojojin nahiyar don kaiwa ga gaci.