Ministan sadarwa na kasar Kamaru da ya yi magana da yawun gwamnatin kasar yace Kamaru kasa ce ta zaman lafiya.
Ministan yayi furucin ne bayan da wata kafa a kasar Amurka ta saka Kamaru a matsayin kasa ta biyu a duniya da ta fi hadari. Wannan bayanin da kafar ta bayar ya batawa gwamnatin Kamaru rai.
Kasar tace tana iyakar kokarinta domin tabbatar da zaman lafiya duk da cigaba da yaki da ta keyi da 'yan Boko Haram a jihar arewa mai nisa dake makwaftaka da Najeriya.
Ministan ya sake komawa kan wata sanarwa da jakadan Amurka a Kamaru ya yi a ranar 16 ga watan Fabrairun wannan shekarar inda ya yi watsi da labaran karya da yace an lakabawa gwamnatin Amurka domin tada zaune tsaye.
Wasu 'yan Kamaru da suka ji labarin sun nuna bakin cikinsu matuka. Suka ce wadanda suka yada wannan labarin sun taba zuwa Kamaru ne ko kuma suna alakanta Kamaru da Afghanistan ne? Suka ce su a Kamaru suna nan lafiya lau kada a tayar masu da zaune tsaye.
Ga karin bayani