Yau laraba Mutane a Brusell sunyi shiru na minti guda domin tunawa da mutane 34 da suka rasa rayukan su a sakamakon harin bomb da aka kai a tashar jirgin kasar.Sai dai kuma kafofin yada labarai sun bayyana cewa an samu cafke wasu mutanen da ake tuhuma da aikata wannan taasar.
Mutane masu nuna alhinin su game da wannan harin dai suna hallarar dandalin nan ne da ake kira PLACE de Bourse dake Brussel din suna ajiye furen kallo.
Duk da irin sanyin da ake yi wannan dandalin ya cika makil da dan mutum.Da farko mutanen sunyi tsam na dan tasawon lokaci kana daga bisani suka barke da tafi alamun cewa suna nuna goyon bayan su.
Daga bisani kuma suka barke da sowar cewa Belgium muna maki fatan yawancin rai, sai kuma aka ci gaba da tafi.
Sai dai rahotanni sun bayyana cewa ‘yan sanda sun bayyana cewa sun kame wanda ake tuhuma da kai wannan harin na jiya, wanda yayi dalilin mutuwar mutane 34.
Sai dai tun farko rahotanni sun Ambato cewa Najim Laachraoui dan shekaru 25 yana ciki jerin mutanen da ake nema game da wannan harin na jiya to sai dai ba tabbacin cewa ko shine aka kame game da harin na jiya.