Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Belklo a firar da ya yi da Muryar Amurka ya shaidawa duniya jihar ta soke tallafin da ake baiwa alhazan jihar dake zuwa aikin hajji a Saudiya.
Gwamnan yace sun tarar ana kashe biliyoyin Nera da sunan bada tallafi ga alhazan jihar amma tallafin nada ayar tambaya. Yace banda kudi da kowane alhaji ke biya gwamnati kuma tana kashe fiye da biliyan biyu kowace shekara. Amma shi wanda ake kashe kudin a kansa bai sani ba. An fake da sunayen alhazai ana diban kudin gwamnati ana watanda dasu. Yace bara sun yi kokarin soke shirin amma bai yiwu ba saboda mutane sun yi kanekane cikin lamarin. Duk da haka sun rage sun kashe miliyan dari tara. Burinsu wannan shekarar shi ne soke shirin gaba daya.
Amma masanin alamuran yau da kullum Alhaji Jibril Iliyasu bai goyi bayan janye tallafin ba. Kamata ya yi gwamnan ya nemi mutane amintattu masu rikon amana, masu adalci da gaskiya ya basu aikin su taimaka ma alhazan kuma su basu tallafin akan lokaci.. Yace tabbas sun san gwamnati na tallafawa amma wasu na anfani da damar su danne tallafin.
Dangane da kamfanonin dake daukan alhazai Alhaji Iliyasu ya gargadi gwamnan ya sa ido akansu ya zauna da kowane kamfani ya tabbatar sun yi abun da yakamata.
Ga karin bayani.