Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Madugun 'yan adawan Uganda na shan kamu cikin daurin talala


Madugun adawan Uganda Kizza Besigye tun bayan da aka gama zaben watan jiya an kamashi sau tara yanzu
Madugun adawan Uganda Kizza Besigye tun bayan da aka gama zaben watan jiya an kamashi sau tara yanzu

Tun lokacin da aka gudanar da zaben Uganda ranar 18 ga watan jiya madugun 'yan tawayen Uganda ke shan yawan kamu daga jami'an 'yansandan kasar

Kimanin wata guda ke nan tunda hukumar 'yansandan Uganda suka yiwa madugun 'yan adawa Kizza Besigye daurin talala bayan zaben shugaban kasa na ranar 18 ga watan Fabrairu.

Tun daga lokacin jami'an 'yansandan kasar sun kama dan adawan sau tara , wato duk lokacin da ya yi yunkurin fitowa daga gidansa.

Amurka da Tarayyar Turai sun sha kiran mahukuntan Uganda da su sako dan adawan ba tare da bata wani lokaci ba. To saidai mai magana da yawun 'yansandan kasar Fred Enanga yace suna tsare da Besigye ne bisa doka.

Fred Enanga yace "kuna sane da dalilan da suka sa rundunar 'yansanda ta dauki matakan hana barkewar tashin hankali a karkashin doka mai lamba 24 ta 'yansanda. Dokar ta ba 'yansanda ikon daukan matakan da zasu hana aukuwar tashin hankali da suka hada da daurin talala idan rundunar tana ta tabbaci cewa barin wani ko wasu suna yawo suna saduwa da wasu zai jawowa jama'a illa ko kuma ya shafi zirga zirgan ababen hawa"

Banda hana Besigye fita 'yansandan sun kuma hana mutane su ziyarci Besigye a gidansa ko kuma su gana dashi. Ko iyalansa ma an takaita saduwarsu dashi. Bugu da kari an hana motoci shiga gidansa

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG