Jihohin Lagos Da Kebbi Sun Rattaba Hannu Akan Bunkasa Noma Da Kasuwanci

INEC

Makasudin rattaba hannu shine domin inganta tattalin arziki masamman kasuwanci da harkar noma

Jihohin Lagos da Kebbi sun rattaba hannu akan yarjejeniyar bukasa noma da kasuwanci a tsakanin su , kuma ana fatan wannan zai bude hanya ga sauran jihohin arewa da nufin inganta kasuwanci da noma duk dai a kokarin jihohin na samo hanyoyin dogaro da kai.

Makasudin rattaba hannu akan wannan yarjejeniya dai kamar yadda Gwamna jihar Kebbi, Alhaji Atiku Bagudu, ya shaidawa ‘yan jarida ciki har da wakilin muryar Amurka Babagida Jibril, jim kadan baya kamala ganawa da Gwamna jihar Lagos, Akinwumi Ambode, yace shine na inganta tattalin arziki masamman kasuwanci da harkar noma.

Gwamna Atiku Bagudu, yace an kara bude kasuwa, na duk abinda mutun keyi jihar Kebbi, domin ya kasance abinda suke samu ta fuskar abinda suke yi ya kara ingantadomin sami Karin arziki kazalika mutanen Lagos, suma su kara samun yelwa da samun arziki na wadannan abubuwa domin hadin kai.

Sai dai kuma a bangaren ‘yan kasuwa masamman na arewacin Najeriya, na ganin akwai bukatar shugabani masamman Gwamnoni su sauna tare da Gwamnatin Lagos, na kawo karshen cin zarafi da suke zargin Gwamnatin jihar tana yi masu ta bangaren kasuwanci kamar yadda Malam Aminu ya shedawa wakilin muryar Amurka.

Your browser doesn’t support HTML5

Jihohin Lagos Da Kebbi Sun Rattaba Hannu Akan Bunkasa Noma Da Kasuwanci - 3'06"