Rundunar ‘yan Sandan jihar Lagos ta fara wani bincike na neman wasu mutane da ake zargi da sace wasu ‘yan mata uku a wata makaranta mazaman kanta Babington Marcurley junior seminary dake garin Ikorodu a jihar ta Lagos.
Su dai wadannan ‘yan mata ‘yan makaranta an ce wasu ‘yan bindiga ne suka shiga makarantar tasu misalign kafe 9.00 na dare suka yin awon gaba dasu.
‘Yan matan da aka sace sune Temilehin , Tofumi da Deborah dukkan su ‘yan aji biyu na babbar makarantar sakadare wato SSS 2, na wannan makaratar haka nan kuma mutanen sun so suyi awon gaba da wani sauratyi shima dan SSS 2 amma hakkan bai yu ba har zuwa wannan lokaci babu duruyar wadannan ‘yan mata da akace an sace da bakin bindiga a makarantar tasu.
Rundunar ‘yan Sandan jihar Lagos da na jihar Ogun sun dukufa neman wadanda suka aikata wannan aika aika.
Hajiya Kaka wata mai rajin kare hakkin mata tayi tir da wannan aika aika tana mai cewa yakamata a hanzarta gano su.
Malam Musa Jika na kungiyar Amnesty support group ya bayana wanna abinda ya faru a matsayin halin rashin tsaro dake ci gaba da gallabar ‘yan Najeriya tare da kira ga Gwamnati da ta dauki kwararan mataikai.
Your browser doesn’t support HTML5