A yau Litinin aka bayyana sakamakon zaben, wanda ya shammaci masu ra’ayin mazan jiya, ciki har da shugaban Majalisar, Ayatollah Mohammed Yazdi, wanda bai kai ga nasara ba.
Wakilan wannan majalisa za su yi wa’adin shekaru takwas a majalisar wacce ita ke da alhakin zaben wanda zai gaji shugaban Addini Ayatollah Ali Khamenei.
Baya ga wannan zabe, masu kada kuri’a sun yi zaben ‘yan majalisun dokokin kasar mai wakilai 290.
Ana sa ran daga yau Litinin zuwa gobe Talata za a fitar da sakamakon zaben.
Sakamakon farko da aka fitar amma ba a hukumance ba, ya nuna cewa masu neman sauyi da masu matsakaicin ra’ayin sun lashe kujeru 30 a Tehran.