Rahotani na cewa rikicin ya taso ne sakamakon takaddama kan wasu wuraren kamun kifi, kuma kawo yanzu daruruwan wadanda lamarin ya shafa na gudun hijira. Domin yanzu haka an sami asarar rayuka da kuma kona gidaje, an dade dai ana rikici kan wuraren wanda ko a baya sai da wata kotu a yankin ta yanke hukunci, amma hakan bai hana rikici ba, inda kowa yake ikirarin mallakar wuraren.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin kakakin rundunar yan Sandan jihar Taraba DSP Josep Kwaji, yace har yanzu dai babu wanda aka kama, amma kuma ana nan ana bincike ga wadanda ke da hannu kan wannan rikici.
Yankin Lau na daga cikin yankunan dake da albarkatun ruwa a jihar Taraba, inda ake noman rani, yayin da kasuwar Masunta ma kan bude, batun da su kansu wanda rikicin ya shafa ke neman tallafi daga gwamnatin jihar.
Domin karin bayani.