Kungiyoyin dai sunyi wannan kukan ne a wani taron manema labarai da suka kira jiya a garin Maiduguri, inda suka nuna rashin jin dadinsu game da matakin da rundunar sojan ta dauka, na rufe musu kasuwarsu dama hanasu yanka a Kwata.
Wanda hakan ka iya jefa su cikin wani hali yanzu haka dai an kwashe kimanin kwanaki 20 kenan, sunce dai basu kadai ne ke amfana da kasuwar da mayankan ba, mutane kan je tun daga Kudancin Najeriya, don sayan dabbobi a kasuwar.
Mutanen wannan kasuwa dai na gudanar da hada hada har da mutanen ketare, amma rufe wannan kasuwa ya haifar musu da cikas, ganin cewa sama da mutane Miliyan 2 ne ke amfana da Mayankar da Kasuwar.
Amma akwai koke koken da ake samu na cewa ana samun dabbobin da ake shigowa da su kasuwar ana sato su ne hannun Fulani, domin kai su mayakar. Amma mataimakin shugaban wannan kasuwa Alhaji Yakuba Gwani, ya musunta wannan zargi.
Ko shakka babu rufe wannan kasuwa da mayanka ya harfar da karancin nama a cikin birnin Maiduguri da kewaye, yayin da jama’a suka karkata wajen yan Kifi da yan Kaji.
Domin karin bayani.